Matakan da majalisar dattawa ta dauka kan dokar zabe

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da sashen dokar da ya wajabta aika sakamakon zabe kai-tsaye daga rumfunan zabe ta hanyar na’ura.
Majalisar ta bayyana cewa aika sakamakon ta na’ura zai zama hanyar farko, amma idan aka samu matsalar intanet, Hukumar Zabe ta kasa (INEC) za ta koma amfani da takardar rubutu wajen aika sakamakon, kamar yadda aka saba a baya.
Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da kudirin a zaman gaggawa da majalisar ta gudanar kan dokar, inda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya amince da shi bayan samun goyon bayan sauran sanatoci.
Bayan haka, majalisar ta kafa kwamiti mai mambobi 12 domin yin aiki tare da Majalisar Wakilai wajen tsefe dokar, kamar yadda tsarin amincewa da dokoki ya tanada.
An kira zaman gaggawar ne bayan da ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyun hamayya suka gudanar da zanga-zanga a harabar Majalisar Dattawa a ranar Litinin, suna nuna adawarsu ga jinkirin wajabta aika sakamakon zaɓe kai-tsaye ta na’ura daga kowace rumfar zabe.





