Kai Tsaye | Rasuwar Mahaifiyar Nasiru El-Rufai

Kai Tsaye | Rasuwar Mahaifiyar Nasiru El-Rufai

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye dangane da rasuwar mahaifiyar Malam Nasiru El-Rufai

LIVE 18 updates
7:54 pm just now

Tambuwal Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga El-Rufai

Tambuwal Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga El-Rufai

Tsohon gwamnan Jihar Sokoto State kuma sanata, Aminu Waziri Tambuwal, ya kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon gwamnan Kaduna State, Nasir El‑Rufai, sakamakon rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai.

Tambuwal ya bayyana cewa ya ziyarci El-Rufai tare da tawagarsa domin jajanta masa da iyalansa a wannan lokaci na jimami. Ya ce rashin uwa babban rashi ne da ke taɓa zuciya, kuma ba abu ne mai sauƙi ba.

Ya kuma yi addu’ar Allah (SWT) Ya gafarta wa marigayiyar, Ya jikanta da rahama, Ya sanya ta cikin Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalanta haƙurin jure wannan babban rashi.

7:28 pm just now

Gwamna Radda Yaje Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyar El-Rufai

Gwamna Radda Yaje Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyar El-Rufai

Gwamnan Jihar Katsina State, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon gwamnan Kaduna State, Nasir El-Rufai, sakamakon rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai.

A yayin ziyarar, gwamnan ya jajanta wa iyalan marigayiyar tare da yin addu’ar Allah (SWT) Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata kura-kuranta, sannan Ya bai wa iyalanta haƙurin jure wannan babban rashi.

7:16 pm 9m ago

Shugaban APC na Ƙasa Ya Ziyarci El-Rufai Domin Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Shugaban APC na Ƙasa Ya Ziyarci El-Rufai Domin Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa

Shugaban jam’iyyar Nentawe Yilwatda na ƙasa ya kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El‑Rufai, a gidansa da ke Abuja.

Ziyarar ta gudana ne domin jajanta masa kan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai, wadda ta rasu ranar Juma’a, 27 ga Maris, 2026, a birnin Cairo na ƙasar Egypt bayan fama da jinya.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana alhininsa kan rasuwar marigayiyar, tare da yi wa iyalan El-Rufai addu’ar Allah Ya jikanta da rahama, Ya kuma ba su juriyar wannan babban rashi.

7:10 pm 15m ago

Iyalan El-Rufai Sun Ƙi Jirgin Gwamnati, Sun Tanadi Nasu Domin Dauko Gawar Hajiya Umma daga Masar

Rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna cewa iyalan Malam Nasir El-Rufai ba su amince da tayin gwamnatin na tura jirgin gwamnati domin ɗauko gawar Hajiya Umma El-Rufai daga ƙasar Masar ba.

A maimakon haka, iyalan sun bayyana cewa sun tanadi nasu jirgi na kashin kansu, wanda ake sa ran zai tashi da yammacin yau Asabar zuwa Masar domin ɗauko gawar marigayiyar.

Rahotannin sun kuma ce za a gudanar da jana’izar ne a birnin Abuja ranar Lahadi, sannan Malam Nasir El-Rufai da iyalansa za su koma Kaduna ranar Litinin domin ci gaba da karɓar gaisuwar ta’aziyya daga ‘yan uwa da abokan arziki.

7:03 pm 22m ago

Malami da Amaechi Sun Ziyarci El-Rufai Domin Ta’aziyya

Tsohon Ministan Shari’a na Ƙasa, Abubakar Malami, SAN, tare da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, sun kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, bisa rasuwar mahaifiyarsa.

Sun kai ziyarar ne domin jajanta masa da iyalansa kan wannan babban rashi, tare da yi masa addu’ar Allah Ya gafarta wa marigayiyar, Ya jikanta da rahama, Ya kuma ba iyalanta haƙurin jure rashin. 🤲

6:35 pm 50m ago

Atiku Abubakar Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Wajen El-Rufai a Kaduna

Atiku Abubakar Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Wajen El-Rufai a Kaduna

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, bisa rasuwar mahaifiyarsa.

Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya ziyarci El-Rufai ne a gidansa da ke Kaduna domin jajanta masa da iyalansa kan wannan babban rashi da ya same su.

2:09 pm 5h ago

Shugaban Kasar Tinubu, ya mika sakon ta’aziyya ga Nasir El-Rufai

Ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai daraja wadda ta raini ‘ya’ya da jikoki da suka bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban ƙasa.

2:01 pm 5h ago

Malam Nasir El-Rufai Ya Fara Karbar Gaisuwa Bayan Rasuwar Mahaifiyarsa

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya fara karɓar gaisuwar ta’aziyya daga abokai, ‘yan uwa da magoya baya bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Umma El-Rufai.

Rahotanni sun bayyana cewa manyan ‘yan siyasa, shugabannin al’umma da kuma magoya bayansa daga sassa daban-daban na ƙasar nan na ci gaba da zuwa domin jajanta masa da iyalansa kan wannan babban rashi da ya same su.

Mutane da dama da suka kai ziyarar ta’aziyyar sun bayyana Hajiya Umma El-Rufai a matsayin mace mai kyawawan halaye, wadda ta rayu cikin sauƙi da taimakon al’umma, tare da addu’ar Allah Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya kuma sanya ta cikin Aljannatul Firdausi.

Iyalin El-Rufai sun gode wa dukkan waɗanda suka nuna alhini da jajantawa a wannan lokaci mai cike da jimami, tare da roƙon al’umma da su ci gaba da yi wa marigayiyar addu’a domin Allah Ya jikanta da rahama.

11:16 pm 20h ago

Bama so inji Bashir El-Rufai Wa Uba Sani

Bashir El-Rufai yace bama so, akan sakon ta’aziyar da Gwamna Uba Sani Ya Wallafa a shafin sa na X.

11:15 pm 20h ago

An Saki Nasir Elrufai

Bello El-Rufai ya bayyana cewa an saki mahaifinsa daga tsarewa da ya kira ba bisa ka’ida ba, ya gode wa jama’a bisa goyon baya.

9:46 pm 21h ago

Atiku Abubakar: Rasuwar Hajiya Umma El-Rufai abin tashin hankali

Atiku ya tuna da marigayiyar a matsayin mace mai imani da hidima ga al’umma, ya kuma roki Allah ya bai wa iyalanta hakuri, Allah kuma yajikanta da rahama.

Ya kara da cewa ya ce rasuwar ta girgiza zuciya, amma rasuwarta ranar Juma’a abin sanyaya zuciya ne ga iyali.

9:02 pm 22h ago

Mutuwar Mahaifiyar El-Rufai ya girgizani inji Nuhu Ribado

Mutuwar Mahaifiyar El-Rufai ya girgizani inji Nuhu Ribado

Nuhu Ribadu ya wallafa a shafin sa cewa mutuwar mahaifiyar Malam Nasiru El-Rufai ya girgizani domin rayuwa da ita a matsayin uwa jajirtaciya.

8:07 pm 23h ago

Ta’aziyya ta rikide zuwa muhawara

Ra’ayoyin Jama’a Sun Rabu Kashi: Yayin da ake jimamin rasuwar Hajiya Umma El-Rufai, mabiya shafukan Gwamna Uba Sani sun mayar da martanin da sakon ta’aziyyar da Gwamna Uba Sani yayi kana cewa thier mother hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin al’umma.

👉 Wasu na kira ga hadin kai, wasu kuma na ganin siyasa ta shigo ciki.

7:51 pm 23h ago

Gwamnar Kaduna Uba Sani Yayi Taaziyya Ga Iyalan El-Rufai

Gwamnar Kaduna Uba Sani Yayi Taaziyya Ga Iyalan El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana alhininsa bisa rasuwar mahaifiyar tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai A shafun sa na Facebook

A cikin sakonsa, ya ce yana mika ta’aziyyarsa ga El-Rufai da daukacin iyalansa bisa wannan babban rashi.

Ya bayyana marigayiya, Hajiya Umma El-Rufai, a matsayin mace mai tausayi, tawali’u da kuma kyawawan dabi’u, wacce ta rayu tana taimakon al’umma tare da bayar da shawarwari masu amfani.

Gwamnan ya kara da cewa marigayiyar ta kasance ginshiki wajen hada kan jama’a da kuma yada kyawawan dabi’un addini da hakuri.

👉 Ya yi addu’ar Allah ya gafarta mata kura-kuranta, ya karbi ayyukanta na alheri, ya kuma saka ta da Aljannatul Firdaus.
🙏 Ya kuma roki Allah ya bai wa iyalanta hakurin jure wannan babban rashi.

6:48 pm Mar 27

Hajiya Fatima Zarah Ahmad ta rasu a Cairo

Hajiya Fatima Zarah Ahmad ta rasu a Cairo

A rahoton da muke samu yanzu Hajiya Fatima Zarah Ahmad ta rasu a Cairo bayan jinya.
Shin El-Rufai zai samu halartar jana izar Mahaifiyarsa ?
Zaku iya rubuta mana Ra’ayinku a shafukan sada zumunta na Hausa360

6:39 pm Mar 27

Acikin Awa Daya Mutane sama da dubu ashirin ( 20000 ) sun jajin ta wa Bello El-Rufai

Acikin Awa Daya Mutane sama da dubu ashirin ( 20000 ) sun jajin ta wa Bello El-Rufai

Mutane sama da dubu shirin ( 20000 ) sun jajin ta wa Bello El-Rufai ackin a wa daya da sanarwar da yayi a shafin sa na Facebook.

6:26 pm Mar 27

Bello El-Rufai Yasanar da Rasuwar Kakarsa

Sanarwar yafito ne daga shafin dan Malam Nasiru El-Rufai, a yau Juma\'a da misalin karfe 4:45 na yamma, ya bukaci al\'umma da su tayasu da addua

5:14 pm Mar 27

Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai Ta Rasu

Mahaifiyar Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai Ta Rasu

Rahotanni sun bayyana cewa Hajiya Umma El-Rufai ta rasu ne a ‘yan sa’o’i da suka gabata, lamarin da ya jefa iyalai da makusanta cikin jimami.

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker