Labarai

Kotu a Seoul Ta Yanke Wa Tsohon Firaministan Koriya ta Kudu Hukuncin Daurin Shekara 23

Wata babbar kotu a Seoul, babban birnin ƙasar Koriya ta Kudu, ta yanke wa tsohon firaministan ƙasar, Han Duck-Soo, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 23, bisa samunsa da laifin hannu a ayyukan tayar da tarzoma.

Laifukan da ake tuhumarsa da su sun samo asali ne daga rawar da ya taka wajen yunƙurin ayyana dokar soji a watan Disamban 2024, a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Yoon Suk Yeol. Rahotanni sun bayyana cewa yunƙurin bai yi nasara ba, amma ya jefa ƙasar cikin rikicin siyasa.

A hukuncin da kotun ta yanke, alkalin shari’ar ya ce an same Han Duck-Soo da laifi ne sakamakon gaza kiran taron majalisar dokoki da kundin tsarin mulki ya tanada kafin a ayyana dokar soji, abin da ya sa aka ɗauki matakin a matsayin saɓa wa doka.

Han Duck-Soo dai ya taɓa rike mukamin shugaban riƙo na ƙasar na tsawon makonni bayan da aka tsige Shugaba Yoon Suk Yeol, kafin a kammala shari’o’in da suka biyo bayan rikicin.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker