Tsaro

Iran ta yi barazana: Za ta kai hari ga sansanonin soji idan aka farmake ta

Gwamnatin Iran ta sanar da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, cewa za ta dauki sansanonin soji da ke yankin Gabas ta Tsakiya a matsayin wuraren da za ta kai wa hari idan aka fara kai mata farmaki.

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa barazanar da Donald Trump ke yi na nuna yiyuwar kai hari a kowane lokaci, duk da cewa Iran ba ta da burin shiga yaki.

Tun da farko, Trump ya bai wa Iran wa’adin kwanaki 10 zuwa 15 domin ta cimma matsaya kan shirinta na nukiliya. Ya kuma gargade ta cewa idan ba a samu yarjejeniya ba cikin wannan lokaci, sakamakon da zai biyo baya ba zai kasance mai sauki ba.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker