Tsaro

Iran Ta Gargadi Kasashen Gabas ta Tsakiya Kan Bai wa Amurka Ko Isra’ila Damar Kai Hari

Iran ta bayyana cewa za ta yi amfani da dukkan karfin sojinta domin kare kanta daga duk wani hari da Amurka ko Isra’ila za su kai mata.

A cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Wajen kasar, Abbas Araghchi, ya fitar, ya ce ya tattauna ta waya da kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Kuwait, Bahrain da Iraƙi. A cewarsa, Iran ta sanar da su cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kanta idan aka kai mata hari.

Araghchi ya kuma tunasar da kasashen da muhimmancin hana amfani da yankunansu ko kayayyakinsu ta hanyar da ba ta dace ba, yana mai nuni da cewa kada su bai wa Amurka ko Isra’ila damar amfani da su wajen ƙaddamar da hari kan Iran.

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker