Labarai

Gwamna Abba Yusuf ya kaddamar da motocin CNG

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci kaddamar da sabbin abubuwan hawa masu amfani da iskar gas na CNG a karkashin shirin gwamnatin tarayya na bunkasa makamashi mai tsafta.

An kaddamar da motocin da babura masu kafa uku da aka tanada domin inganta tsarin sufuri mai sauki, araha da kuma kare muhalli daga gurɓatawa a jihar Kano.

Gwamnatin ta bayyana cewa shirin na daga cikin kokarin rage dogaro da fetur tare da saukaka wa al’umma halin tsadar sufuri a fadin jihar.

Wannan mataki na kuma da nufin inganta amfani da makamashi mai tsafta da dorewa a Najeriya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker