Gobara Ta Kone Keke Napep 17 Da Tankokin Dakon Mai Biyu A Kano

Akalla babura masu kafa uku na Keke Napep 17 da tankokin dakon mai biyu ne suka ƙone sakamakon gobarorin da suka tashi a wasu gidajen mai a Jihar Kano.
Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
A cewarsa, gobarar farko ta tashi ne a gidan mai na AA Ayagi da ke kauyen Kanye, a kan titin Gwarzo, cikin karamar hukumar Kabo, da misalin ƙarfe 8:45 na dare ranar Talata.
Ya ce hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 20:45 daga wani jami’inta, Muhammad Wada Abdulsalam, wanda ya bayar da rahoton tashin gobara a gidan man.
“Da isowar jami’anmu daga sashen Rijiyar Zaki, sun tarar da wata tankar mai mallakar Kamfanin AA Ayagi tana ci da wuta yayin da ake sauke man fetur,” in ji Abdullahi.
Ya bayyana cewa a lokacin tashin gobarar, an riga an sauke mai daga bangarori biyu na tankin karkashin ƙasa, yayin da ake ƙoƙarin sauke ragowar kimanin lita 5,000 na man fetur. Gobarar ta lalata tankar gaba ɗaya.
A wani lamari na biyu, gobara ta tashi a tashar mai ta Al-Wahida Nigeria Limited da ke Rimin Kebe Karshen Kwalta, cikin karamar hukumar Nassarawa. A nan ma, wata tankar mai mallakar Kamfanin BA Bello, wadda ke dauke da kimanin lita 45,000 na man fetur, ta kama da wuta yayin da ake sauke kayan.
Abdullahi ya ce gobarar ta lalata kan motar tankar da wani bangare na jikin ta, tare da kone Keke Napep guda 17 (Adaidaita sahu) da ke kusa da wurin.
Sai dai ya tabbatar da cewa, da taimakon Allah, jami’an hukumar sun shawo kan gobarar tare da hana ta yaduwa, inda aka samu ceto ragowar man fetur da kuma wasu sassan tankar.
A gefe guda, wata gobara ta sake tashi a Kundila Quarters, kusa da Makarantar SALSA, inda ta lalata ɗaki ɗaya, bandaki ɗaya, da kuma wata hanya a cikin wani ginin gidaje.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Sani Anas, ya yi kira ga jama’a—musamman masu tashoshin mai da direbobin tankokin dakon mai—da su rika bin ka’idojin kare hatsari yayin sauke man fetur domin kauce wa irin wadannan afkuwan.





