LabaraiSiyasa

Ba Zan Koma APC Ba Sai An Fayyace Matsayina da Na Magoya Bayana — Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba zai koma jam’iyyar APC ba matuƙar ba a fayyaɗa masa matsayinsa a cikin jam’iyyar, tare da dawo da takardun manufofin da aka tsara domin inganta rayuwar talakawan Najeriya.

Kwankwaso ya jaddada cewa duk wata shawara da zai yanke dole ne ta yi la’akari da matsayinsa, na magoya bayansa, da kuma matsayin gwamnatin jihar Kano a cikin tsarin jam’iyyar da ake maganar komawa cikinta.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Miller Road a Kano, yayin da yake karɓar shugabanni da magoya baya daga ƙananan hukumomin Rano da Dawakin Tofa, tare da wasu mambobin tafiyar Kwankwasiyya da suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar NNPP.

“Idan har zan koma APC, dole ne a bayyana mini matsayina a cikin jam’iyyar. Haka kuma, sai an sanar da mu abin da ke jiranmu, sannan mu san matsayin jihar Kano da magoya bayanmu,” in ji Kwankwaso.

Ya ce babban burinsa shi ne kare muradun al’umma, musamman talakawa, tare da tabbatar da cewa duk wata tafiya ta siyasa za ta amfani jama’a da magoya bayansa, ba wai mutane kaɗan ba.

Wannan furuci na Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta yaɗa raɗe-raɗin yiwuwar sauya sheƙar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker