Siyasa

Atiku ya roki INEC ta sake duba ranar zaben 2027

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) da ta sake nazarin ranar da aka tsayar domin gudanar da babban zaben 2027, yana mai cewa lokacin ya yi daidai da watan Ramadan.

A ranar Juma’a, INEC ta sanar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a ranar 20 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi zai gudana a ranar 6 ga Maris, 2027.

Da yake mayar da martani cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), Atiku ya ce ranar 20 ga Fabrairu ta faɗo a tsakiyar watan Ramadan, lokacin da miliyoyin Musulmin ƙasar ke gudanar da azumi da ibada.

Ya ce sanya irin wannan muhimmin al’amari na kasa a lokacin ibada na nuna rashin la’akari da halin zamantakewa da addini na al’ummar kasar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa ya zama wajibi a yi la’akari da bambancin al’ummomi da al’adun da ke cikin Najeriya kafin yanke irin wadannan muhimman shawarwari da suka shafi rayuwar ‘yan kasa.

Sai dai INEC ta bayyana cewa an zabi ranakun zaben ne bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker