Siyasa

APC Ta Zabi Sabbin Shugabanninta

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta zabi sabbin shugabannin da za su jagoranci harkokin jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.

An bayyana sabbin shugabannin ne a yayin babban taron ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar ranar Juma’a a birnin Abuja, inda wakilai daga sassa daban-daban na ƙasar suka halarta.

A yayin taron, jam’iyyar ta tabbatar da Farfesa Nentawe Yilwatda, wanda ke rike da mukamin shugaban riƙo a baya, a matsayin cikakken Shugaban Jam’iyyar na ƙasa. Haka kuma an tabbatar da Sanata Surajudeen Ajibola Basiru a matsayin Sakataren Jam’iyyar na ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa yawancin shugabannin da aka zaɓa sun samu mukamansu ne ta hanyar masalaha (consensus), wata hanya da jam’iyyar ta fi amfani da ita wajen cimma matsaya tsakanin ‘ya’yanta.

Jerin Sabbin Shugabannin APC

  • Shugaban Jam’iyya na ƙasa: Farfesa Nentawe Yilwatda
  • Mataimakin Shugaba (Arewa): Ali Bukar Dalori
  • Mataimakin Shugaba (Kudu): Dr. Benjamin Obi Nwoye
  • Sakataren Jam’iyyar na ƙasa: Sen. Surajudeen Ajibola Basiru
  • Mataimakin Sakatare: Prof. AbdulKarim Abubakar Kana
  • Babban Lauyan Jam’iyya: Murtala Aliyu Kankia
  • Babban Ma’aji na ƙasa: Uguru Mathew Ofoke
  • Babban Sakataren Kuɗi: Amb. Haruna Ginsau
  • Babban Sakataren Tsare-tsare: Muhammad Sulaiman Argungu, OFR
  • Sakataren Walwawa: Donatus Enyinnah Nwankpa
  • Sakataren Yaɗa Labarai: Felix Morka
  • Babban Mai Binciken Kuɗi: Sen. Abubakar Maikafi
  • Shugabar Mata: Dr. Mary A. Idele
  • Shugaban Matasa: Dayo Israel

KARANTA: Manyan Jiga-Jigan APC Sun Hallara A Babban Taron Jam’iyya A Abuja

Ana sa ran sabbin shugabannin za su jagoranci jam’iyyar wajen tsara dabarun siyasa da shirye-shiryen da za su tunkari manyan zaɓuɓɓukan siyasa masu zuwa a Najeriya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker