Tsaro

Ana zargin Lakurawa sun kashe akalla mutum 30 a hare-hare a Kebbi

Wasu ’yan bindiga da ake zargin suna da alaka da Kungiyar Lakurawa sun kashe akalla mutum 30 tare da lalata kauyuka bakwai a hare haren da suka kai a yankin arewa maso yammacin Jihar Kebbi, kamar yadda jami’an tsaro suka shaida wa AFP a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, Bashir Usman, ya ce maharan sun kai farmakin ne a yankin Bui na Karamar Hukumar Arewa da misalin ƙarfe 1:15 na rana a ranar Laraba.

Rahoton da kamfanin dillancin labaran ya gani ya nuna cewa adadin wadanda suka mutu ya haura mutum 30, ciki har da mutanen da suka fito daga kauyukan Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal da Dan Mai Ago domin kare kansu daga harin.

Wani mazaunin ƙauyen Kanzo ya bayyana cewa sun ji karar harbe harbe yayin da suke cikin gidajensu, lamarin da ya sa mutane suka rika tserewa domin neman mafaka, inda harsasai suka samu wasu daga cikinsu.

Jami’an tsaro sun kuma ce maharan sun kwashe shanu da dama a lokacin farmakin.

Bayan harin, an tura jami’an tsaro, sojoji da kuma ’yan sa kai zuwa yankin domin shawo kan lamarin da kuma maido da zaman lafiya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker