Labarai

Amurka Ta Ba Najeriya Tallafin Kayan Aikin Soji Don Ƙarfafa Yaƙin Tsaro

Rundunar sojin Amurka da ke kula da ayyukanta a nahiyar Afirka (AFRICOM) ta sanar da bai wa Najeriya tallafin kayan aikin soji domin ƙarfafa yaƙin da ake yi da matsalolin tsaro a ƙasar.

Rundunar ta bayyana hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata, inda ta ce dakarun Amurka sun sauke muhimman kayan aikin soji a birnin Abuja domin tallafa wa abokan hulɗarsu na Najeriya.

A cewar sanarwar, “Wannan tallafi zai taimaka wa Najeriya wajen inganta ayyukanta na tsaro, tare da ƙara jaddada kyakkyawar alaƙar tsaro da ke tsakanin Amurka da Najeriya.”

Sanarwar ta kuma zo ne tare da hoton wani jirgin dakon kaya da ƙofarsa a buɗe, yayin da ake iya hango kayan aiki jibge a kusa da jirgin. Sai dai ba a bayyana dalla-dalla irin kayan da aka kawo ko adadinsu ba.

Najeriya dai na fuskantar manyan ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da rikicin Boko Haram a arewa maso gabas, ayyukan ƴan bindiga a arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, da kuma tashe-tashen hankula da ƴan aware ke haddasawa a kudu maso gabas.

A wani ɓangare na ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci, Amurka ta bayyana cewa a ranar 25 ga Disambar 2025 ta kai hare-hare kan ƴan bindiga da ke da alaƙa da ƙungiyar IS a jihar Sokoto. Ko da yake ba a fitar da cikakken bayani kan sakamakon harin ba, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana hare-haren a matsayin “masu ƙarfi da haɗari”.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker