Addini

Najeriya Ta Kaddamar Da Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki

Mataimakin shugaban Nigeria, Kashim Shettima, ya jagoranci bikin kaddamar da fara jigilar alhazan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin bana.

An gudanar da bikin ne a Abuja, babban birnin ƙasar, inda jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar aikin hajji suka halarta.

Rahotanni sun bayyana cewa maniyyata kusan 500 ne suka fara tashi zuwa ƙasa mai tsarki tun a yammacin Lahadi a matakin farko na jigilar alhazan bana.

Hukumomin kula da aikin hajji sun bayyana cewa gwamnati na ci gaba da ɗaukar matakai domin tabbatar da nasarar aikin jigilar, musamman ganin ƙalubalen tsadar makamashi da kamfanonin jiragen sama ke fuskanta a halin yanzu.

Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya, Ismail Abba Yusuf, ya bayyana cewa ana aiki tare da hukumomi da kamfanonin jiragen sama domin tabbatar da cewa aikin jigilar alhazai ya gudana cikin sauƙi da tsari.

Ya kuma jaddada ƙudirin gwamnati na tabbatar da jin daɗi da walwalar alhazai tun daga tashinsu daga Najeriya har zuwa sauke farali a ƙasa mai tsarki.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker