Labarai
El-Rufai Ya Isa Kotun Kaduna Domin Ci Gaba da Shari’ar ICPC

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya isa Babbar Kotun Jihar Kaduna domin ci gaba da shari’ar da ake yi da shi.
Hukumar Yai da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission (ICPC), ce ta shigar da ƙarar, inda ake sauraron shari’ar a kotun.
Bayan zaman kotun a Babbar Kotun Jihar Kaduna, ana sa ran a ci gaba da sauraron batun bayar da beli a Federal High Court of Nigeria da ke kusa da wurin.
Karanta Nasir El-Rufai ya maka ICPC a kotu
Ana ci gaba da jiran yadda shari’ar za ta kasance yayin da kotu ke sauraron ƙorafe-ƙorafen da ke gaban ta. 📰





