Siyasa

Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya sauya sheka zuwa APC

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance.

A jawabin da ya yi wa al’ummar jihar ranar Juma’a, gwamnan ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne tare da duka mambobin majalisar zartarwarsa da kuma manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar, kamar yadda kafofin yada labarai na kasar suka ruwaito.

Sauya shekar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ganin wasu gwamnoni da manyan ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa suna komawa APC mai mulki a Najeriya.

Har zuwa yanzu, babu wani cikakken martani daga shugabannin PDP na kasa kan matakin da gwamnan ya dauka.

A kwanakin baya ne kuma Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki jihar Adamawa, inda ya kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Fintiri ta aiwatar matakin da wasu masu sharhi ke ganin kamar wani yunkuri ne na karfafa alakar siyasa tsakanin bangarorin biyu.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Duba
Close
Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker