Kisan Gilla a Kano: Wasu da Ake Zargin Yan Daba Sun Hallaka Matar Aure da Yayanta Shida a Dorayi

Al’ummar unguwar Dorayi Chiranchi a birnin Kano sun shiga jimami bayan wasu da ake zargin yan daba sun kai hari gidan wani mazaunin unguwar, inda suka kashe matar aure da yayanta shida da sanyin safiyar ranar Asabar.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun afkawa Fatima Abubakar mai shekaru 35 tare da ƴaƴanta shida a gidansu da ke Dorayi Charanchi/Gidan Kwari, inda suka yi amfani da muggan makamai suka jikkata su matuƙa.
Ƴaƴan da lamarin ya rutsa da su sun haɗa da Maimuna (shekara 17), Aisha (16), Bashir (13), Abubakar (10), Faruk (7), da Abdussalam wanda ke da kusan shekara ɗaya da rabi a duniya.
Wata sanarwa da kakakin rundunar yansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta ce an garzaya da wadanda lamarin ya shafa zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
Wani mazaunin unguwar, Kabiru Ibrahim, ya bayyana lamarin a matsayin abin girgiza, yana mai cewa al’umma na cikin rudani da alhini sakamakon yadda aka hallaka iyali gaba ɗaya ba tare da sanin dalili ba.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, CSP Kiyawa ya ce Kwamishinan Ƴansandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike, inda Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) ya fara farautar waɗanda suka aikata laifin.
Rundunar ƴansandan jihar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da al’ummar Dorayi baki ɗaya, tare da tabbatar wa jama’a cewa za a gano masu hannu a wannan mummunan aiki domin tabbatar da adalci.





