Labarai

Dalilin Sakin Ƴan Fashin Daji: Gwamnatin Katsina Ta Yi Bayani Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana dalilan da suka sa take la’akari da sakin wasu mutanen da ake zargi da kasancewa ƴan fashin daji, waɗanda hukumomi suka kama a baya, a wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya da wasu al’ummomin jihar suka cimma da ƴanbindiga.

Rahotanni sun ruwaito cewa ana shirin sakin kimanin ƴan fashin daji 70 da ake tsare da su bisa zargin fashi da makami da garkuwa da mutane. Sai dai kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Hon. Nasiru Mu’azu, ya ce har yanzu ba a kammala tantance adadin waɗanda za a saki ba.

A cewarsa, matakin sakin mutanen na daga cikin sharuɗɗan yarjejeniyar sulhu da al’ummomi suka cimma da ƴanbindigar a yankunansu, domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Sharuɗɗan Yarjejeniyar Sulhu

Kwamishinan ya bayyana cewa yarjejeniyar sulhun ta ƙunshi wasu sharuɗɗa da bangarorin biyu suka amince da su, ciki har da:

  • Bai wa ƴanbindigar damar shiga kasuwanni domin saye da sayarwa
  • Ba su damar zuwa asibitoci domin neman magani
  • Ba su damar zirga-zirga ba tare da tsangwama ba
  • Yin cuɗanya da jama’a
  • Daina kai hare-hare a garuruwa da ƙauyuka
  • Daina sace mutane domin kuɗin fansa
  • Sakin mutanen da ake garkuwa da su
  • Sakin ƴanbindigar da ke hannun hukumomi

Ya ce an aiwatar da yawancin sharuɗɗan, kuma yanzu an kai matakin sakin ƴanbindigar da ake tsare da su.

Dalilin Shiga Tsakani

Nasiru Mu’azu ya ce gwamnatin jihar ta shiga cikin wannan tsari ne sakamakon zaman lafiya da aka samu bayan sulhun. Ya jaddada cewa duk da cewa gwamnati ta sha cewa ba za ta yi sulhu kai tsaye da ƴanbindiga ba, ba ta hana al’ummomi yin hakan domin kare rayukansu da dukiyoyinsu.

A cewarsa, yarjejeniyar ta kawo sauƙi sosai, inda wasu ƙananan hukumomi suka shafe kusan shekara guda ba tare da hare-haren ƴanbindiga ba. Ya ce ƴanbindigar sun saki sama da mutum 1,000 tun bayan fara yarjejeniyar, abin da ya ce babban ci gaba ne da ya dace gwamnati ta girmama alkawarin da aka yi.

Tsarin Tantance Waɗanda Za a Saki

Kwamishinan ya bayyana cewa kwamitocin sulhu na ƙananan hukumomi ne ke tattara sunayen ƴanbindigar da ake tsare da su. Bayan kammala tattara sunayen, za a miƙa su ga gwamnati, wadda za ta kai su gaban kotu domin duba su bisa doka kafin a aiwatar da sakin.

Batun Ajiye Makamai

Dangane da fargabar da ake nunawa kan rashin saka sharaɗin ajiye makamai, kwamishinan ya ce za a bi wannan mataki ne sannu a hankali. Ya bayyana cewa akwai dalilai na tsaro da suka sa ba a tilasta ajiye makamai kai tsaye ba, musamman ganin yadda makiyaya ke buƙatar kare dukiyoyinsu.

A ƙarshe, gwamnatin jihar Katsina ta ce tana ganin sulhun ya kawo alfanu mai yawa, kodayake ta amince cewa har yanzu akwai ƙalubale a wasu yankuna, inda ake buƙatar ƙarin kulawa domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga
WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group
Twitter : Hausa360 Twitter
Facebook: Hausa360 Facebook
Instagram : @Hausa360
YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Labarai masu alaƙa

Back to top button

Adblock Detected

Please enable adblocker