Kwankwaso Ya Umurci A Bai Wa Ya’yan Marigayan Yan’ Majalisa Tikitin Takarar Maye Gurbi

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayar da umarnin ba wa ’ya’yan wasu mambobin majalisar dokokin jihar Kano guda biyu da suka rasu damar tsayawa takara don maye gurbin iyayensu.
Wannan mataki ya shafi mazaɓun ƙananan hukumomin Ungogo da Municipal ne a majalisar dokokin jihar.
Yadda Aka Cimma Matsayar
Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Dr. Hashim Sulaiman Dungurawa, ya tabbatar da wannan labari a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai. Ya bayyana cewa an cimma wannan matsayar ne bayan da Sanata Kwankwaso ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar tare da iyalan mamatan a gidansa da ke Kano.
Matasan da aka amince wa su tsaya takarar sune:
- Sa’ad Aminu Sa’ad (Domin wakiltar ƙaramar hukumar Ungogo).
- Nabil Aliyu Daneji (Domin wakiltar ƙaramar hukumar Municipal).
Dr. Dungurawa ya bayyana cewa an ba wa waɗannan matasa damar ne duba da irin gagarumar gudunmawa da kishin ƙasa da iyayensu suka nuna wajen yi wa al’ummar mazaɓunsu hidima lokacin suna raye.
Jam’iyyar ta bayyana fatan cewa Sa’ad Aminu Sa’ad da Nabil Aliyu Daneji za su ɗura daga inda iyayensu suka tsaya, sannan su kwatanta irin adalci da jajircewa da iyayen nasu suka yi fice da shi a fagen siyasa da kuma aikin jinƙan al’umma.





