Rundunar sojojin Najeriya ta musanta rahotannin da ke yawo cewa hare-haren da ta kai a jihar Neja sun yi sanadin mutuwar fararen hula.
Sojojin sun bayyana cewa bayanan da ake yadawa ba su da tushe, tare da jaddada cewa dukkan ayyukan da suke gudanarwa suna bin ka’idojin kare rayukan jama’a.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce hare-haren sun kasance ne kan wasu da ake zargin masu aikata laifuka da suka addabi yankunan jihar.
Ta ce kafin kai hare-haren, ana gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da cewa an kai farmakin ne ga wadanda ake nema kawai, ba tare da cutar da marasa laifi ba.
Sojojin sun kuma ce wasu rahotanni da ake wallafawa na iya zama kokarin bata musu suna da rage amincewar jama’a ga ayyukan tsaro da suke yi a sassa daban-daban na kasar.
Karanta cikakken labarin: NNPC ta kammala aikin bututun gas a Kogin Neja
Rundunar ta bukaci al’umma da su rika tantance bayanai kafin yada su, musamman wadanda suka shafi harkokin tsaro.
Hakazalika, ta jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da suka dace domin dawo da zaman lafiya da tabbatar da kariyar rayuka da dukiyoyin al’umma a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
