Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kashe Amarya A Farawa

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 22 ta yanke wa wani matashi, Shu’aibu Abdulkadir, hukuncin kisa bayan samunsa da laifin kashe amarya Rumasa’u a gidanta da ke Farawa a Jihar Kano. Mai Shari’a Farida Dan Baffa ce ta yanke hukuncin bayan ta gamsu da shaidun da lauyan gwamnati ya gabatar.

Lamarin dai ya faru ne a shekarar 2025, lokacin da Shu’aibu ya je gidan marigayiya Rumasa’u da ke Farawa. An zarge shi da kashe ta bayan ta sanar da shi cewa tana dauke da juna biyunsa shi ya mata ciki. Sai kuma ta nemi ya ba ta Naira 500,000 ko kuma ta fallasa lamarin.

Mai Shari’a Farida Dan Baffa ta yanke hukuncin ne bayan ta gamsu da shaidun da lauyan gwamnati, Barista Bashiru Kabiru Aliyu, ya gabatar mata. Kotun ta saurari shaidu uku da bangaren gwamnati ya gabatar.

Wanda ake kara ya kare kansa a gaban kotun kafin a yanke masa hukuncin kisa. Duk da kokarin da ya yi na kare kansa, kotun ta same shi da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa.

Wannan hukuncin ya sake jaddada tsananin dokokin Najeriya kan laifukan kisan kai. Kotun ta nuna cewa ba za ta yi hakuri da masu aikata irin wadannan laifuka ba. Hukuncin kisa ga Shu’aibu Abdulkadir zai zama gargaɗi ga sauran masu tunanin aikata irin wannan laifi.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

  • Popularly known as Yahmis Yahaya a Media Technology Professional and Journalist with extensive experience in digital media, broadcasting technology, streaming services, and online publishing. He specializes in leveraging technology to enhance news production, content distribution, and audience engagement. As the Founder of Hausa360 Media and a media technology practitioner, he is passionate about digital journalism, technology reporting, media innovation, and the use of emerging technologies to strengthen information access and public communication.

Exit mobile version