Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya bayyana damuwarsa kan ƙalubalen tattalin arziki da ƙasar za ta iya fuskanta a nan gaba, tare da yin tsokaci kan alaƙarsa da Firaministansa, Ousmane Sonko.
Shugaba Faye ya yi kira ga ƴan ƙasar da su kasance cikin shiri domin fuskantar mawuyacin hali, musamman dangane da yiwuwar hauhawar farashin kayayyaki, man fetur da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
A yayin jawabin nasa, shugaban ya kuma nesanta kansa daga wasu matakai da dabi’un Firaminista Sonko, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata.
Faye ya zargi Sonko da ƙoƙarin gudanar da wasu harkoki ba tare da cikakken daidaito da shugabancin ƙasa ba, yana mai nuni da batun gyaran dokokin zaɓe da aka gabatar a majalisar dokokin ƙasar.
Majalisar dai ta amince da wasu daga cikin sauye-sauyen dokokin, yayin da magoya bayan jam’iyyar PASTEF ke ganin hakan na iya bai wa Sonko damar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2029.
Shugaba Faye ya kuma bayyana cewa ya fara tattaunawa da ɓangarorin adawa, yana mai cewa idan Firaministan ya kasa sauke nauyin da ke kansa yadda ya kamata, kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi damar ɗaukar matakin sallamarsa daga mukami.
