Fasinjojin Da Aka Sace Sun Kubuta Bayan Barcin Yan Bindiga

Wasu daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Itobe zuwa Ajegwu Anyigba da ke karamar hukumar Ofu a jihar Kogi sun samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa bayan maharan sun yi barci a cikin dajin da suke tsare da su.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun tare wasu motocin haya guda biyu tare da yin awon gaba da matafiya da ke cikinsu.

Haka kuma an ce sun sace wani direban babur a yayin harin da aka kai ranar Asabar.

Bayan aukuwar lamarin, jami’an tsaro tare da masu sintiri da mafarauta sun bazama domin bin sawun maharan, sai dai ba a samu nasarar cafke su nan take ba.

Sai dai cikin sa’o’i kadan bayan harin, jami’an tsaro sun kama wani mutum mai suna Monday Agi bisa zargin yana da hannu a satar mutanen.

A yanzu haka yana tsare a hannun yansanda yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda ake zargi.

Wasu daga cikin mutanen da suka kubuta, ciki har da Micheal Adejo da Mariam Yakubu, sun bayyana cewa sun samu damar tserewa ne bayan sun lura masu garkuwar sun fada barci.

Sun ce maharan sun kai kusan mutane goma dauke da bindigogin AK-47 da kuma Pump Action, inda suka kwace musu kudade, wayoyi da sauran kayayyaki masu muhimmanci kafin su tafi da su cikin daji.

Daya daga cikin wadanda suka tsere ya bayyana cewa sun yi anfani da lokacin da maharan suka yi barci wajen yin rarrafe a hankali daga wurin da ake tsare da su, kafin daga bisani su isa wani kauye cikin aminci.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version