NSCDC Ta Yi Alkawarin Kawo Karshen Rikicin Manoma

Hukumar Tsaro da Kare Lafiyar Jama’a ta Najeriya (NSCDC) ta bayyana kudurinta na kawo karshen rikicin manoma da makiyaya da ke kara kamari a wasu sassan kasar.

Kwamandan NSCDC na Babban Birnin Tarayya (FCT), Dakta Olusola Odumosu, ya jaddada aniyar hukumar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, musamman wajen shawo kan rikice-rikicen manoma da makiyaya.

Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da kungiyar masu sasanta rikicin makiyaya da manoma (Herders-Farmers Dispute Resolution Volunteers) ta kai masa a Abuja.

Odumosu ya ce kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma muhimman kadarorin kasa na daga cikin abubuwan da ba za a yi wasa da su ba, yana mai kira ga kara hadin gwiwa da al’umma domin samun sahihan bayanan sirri cikin lokaci.

Ya yi nuni da wasu rikice-rikice da suka faru a yankunan Kwali da Gwagwalada da sauran kananan hukumomi na FCT, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dabbobi, yana mai bukatar daukar matakan kariya cikin gaggawa.

Kwamandan ya jaddada cewa dole ne a daina zargin wata kabila ko rukuni, yana mai cewa duk wanda ya aikata laifi makiyi ne ga kasa, kuma za a dauki mataki mai tsauri a kansa.

Ya kuma bukaci zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin manoma da makiyaya, tare da kara wayar da kan jama’a kan muhimmancin rayuwa cikin hadin kai.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar, Mustafa Suleiman, ya yaba wa NSCDC bisa kokarin da take yi wajen magance rikice-rikice daga matakin kasa zuwa na kasa baki daya, yana mai cewa kungiyarsu na kokarin samar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa da hulda da al’umma.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version