Majalisar Wakilai ta Najeriya ta ci gaba da bincike kan sama da dala biliyan 4.6 da aka samu daga tallafin kasashen waje tsakanin 2021 zuwa 2025 domin yaki da cututtuka irin su HIV/AIDS, tarin fuka da zazzabin cizon sauro.
Shugaban kwamitin majalisar kan cututtuka masu yaduwa, Amobi Godwin Ogah, ne ya jagoranci zaman binciken a Abuja ranar Laraba, inda ya ce manufar ita ce tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen amfani da kudaden tallafi.
Tallafin ya hada da dala biliyan 1.8 daga Global Fund da kuma dala biliyan 2.8 daga USAID, wanda aka ware domin inganta tsarin kiwon lafiya da yaki da cututtuka a Najeriya.
Ogah ya ce binciken ba na cin zarafin kowa ba ne, sai dai domin tabbatar da cewa an yi amfani da kudaden yadda ya kamata da kuma dawo da amincewar abokan hulda na kasa da kasa.
Ya kuma ce Majalisar za ta fara bukatar dukkan masu karbar tallafi da masu aiwatar da ayyuka su gabatar da tsare-tsaren su domin amincewar majalisa, tare da rahotanni kowane kwata na shekara.
A cewarsa, wannan mataki zai taimaka wajen inganta sa ido da kuma hana barnatar da dukiyar jama’a.
Ya bayyana damuwa kan yiwuwar Najeriya ta kasa cimma burin kawar da manyan cututtuka nan da 2030, amma ya bukaci ci gaba da kokari da amfani da albarkatun da ake da su yadda ya kamata.
Taron ya samu halartar jami’an Ma’aikatar Lafiya, wakilan Global Fund da sauran kungiyoyin da ke aiwatar da ayyukan tallafi a fannin lafiya.
