Gwamnatin Jihar Filato karkashin jagorancin Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ta samu gagarumar nasara ta hanyar shirin bayar da maganin maciji kyauta. An yi nasarar warkar da mutane 311 daga cikin 312 da macizai suka ciza tsakanin watan Disamba 2025 da Yuni 2026.
Bayan amfani, karbar da rarraba maganin Echitab® Anti-Snake Venom zuwa cibiyoyin lafiya a kananan hukumomi 15, mazauna yankin sun sami saukin samun magani ba tare da matsalar kudi ba.
Wannan shiri ya kara wa jama’a karfin gwiwa wajen neman magani, ya rage mace-macen da akeyi sanadin cizon maciji, kuma ya inganta ayyukan gaggawa a fadin jihar plato.
Yayin da lokacin noma ke gabatowa, lokacin da ake yawan samun cizon macizai, Gwamna Mutfwang ya sake amincewa da siyan karin maganin maciji don rarraba wa a fadin jihar.
Karin Sayan maganin na nufin tabbatar da cewa cibiyoyin lafiya suna da isasshen magani kuma a shirye suke don magance matsalolin cizon macizai cikin gaggawa, tare da tabbatar da ci gaba da samar da magani ga al’umma.
Wannan shiri na nuna jajircewar Gwamnatin Jihar Filato wajen inganta ayyukan lafiya na gaggawa, rage mace-macen da ake yi, da inganta rayuwar al’umma. Gwamnatin ta nuna aniyar ta na samar da ayyukan kiwon lafiya masu inganci ga al’ummar jihar.
