Labaran Safe Na Yau Juma’a 26 Yuni 2026 Hausa360

Saurari cikakken Labaran Safe Na Yau Juma’a 26 June 2026 Hausa360

Wasu manoma sun koka kan yadda tallafin noma da gwamnatoci ke bayarwa ke jinkiri wajen isa hannunsu, lamarin da suka ce na rage musu amfani a lokacin damina. Wani ƙaramin manomi daga Jihar Kano, Malam Habibu Ja’afar Madobi, ne ya fitar da sanarwar a madadin ƙananan manoma. Ya ce tallafi ko rancen kayan noma ba sa isa hannun manoma sai bayan damina ta yi nisa. Ya bukaci gwamnati ta rika tsara rabon tallafin tun kafin damina ta fara.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya kai wa Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, Autan Bawo, ziyarar girmamawa a fadarsa da ke Rano. Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya fitar da sanarwar. Kwamishinan ya yaba da goyon bayan Masarautar Rano ga hukumomin tsaro. Sarkin Rano ya yaba da jagorancin Kwamishinan tare da tabbatar masa da ci gaba da goyon baya.

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta haramta tsarin Almajiranci baki daya. Ya yi magana ne a Abuja yayin taron inganta rayuwar dan Adam a Arewacin Najeriya. Ya ce tsarin na ci gaba da zama babban abin da ke haddasa karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma ta’azzarar matsalolin tsaro. Ya kiyasta cewa yara miliyan 18.3 ne a halin yanzu ba sa zuwa makaranta.

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ba kungiyar ECOWAS shawara kan kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso da suka fice daga cikinta. Ya yi wannan kiran ne a wani taron lacca da cibiyar nazarin shari’a da dimokuradiyya ta kasa (NILDS) ta shirya a Abuja. Ya ce ficewar ƙasashen Sahel guda uku ya raunana haɗin kan yankin da tsaro. Ya bayyana Nijar a matsayin muhimmin gurbi na kariya tsakanin Najeriya da barazanar ‘yan ta’adda.

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta dage sauraron shari’ar neman soke rijistar wasu jam’iyyun adawa zuwa ranar 7 ga Yulin 2026. Kotun ta sauya ranar sauraron shari’ar daga 25 ga Yuni domin bai wa bangarorin da ke cikin ƙarar damar gabatar da takardunsu. Lauyan Accord, Musibau Adetunbi (SAN), ya shaida wa kwamitin alkalai uku cewa an samu kundin shari’ar.

Gwamnatin Jihar Kano ta fara gyaran dokar Hukumar Kwashe Shara ta Kano, REMASAB, domin ba ta damar sarrafa shara zuwa taki da sauran kayayyakin amfani. Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Abubakar Ahmad, ne ya fitar da sanarwar. Shugaban hukumar, Dakta Muhammad S. Khalil, ya ce dokar da aka kafa a 2003 ta mayar da hankali kan tattarawa da zubar da shara kawai. Hon. Musa Ali Kachako ya ce majalisar za ta goyi bayan gyaran.

Arsenal na son ɗauko ɗan wasan Brazil Bruno Guimaraes daga Newcastle a wannan kaka. Tottenham ta sake yin wasi da tayin ɗan wasan Newcastle Sandro Tolani kan Euro miliyan ɗari. RB Leipzig ta ƙi amincewa da tayin da Liverpool ta yi na fam miliyan 100 kan ɗan wasan Ivory Coast Yan Diomande. Mai tsaron ragar Man United, Andre Onana, na shirin rattaba hannu kan kwantaragi a Turkiya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

  • Popularly known as Yahmis Yahaya a Media Technology Professional and Journalist with extensive experience in digital media, broadcasting technology, streaming services, and online publishing. He specializes in leveraging technology to enhance news production, content distribution, and audience engagement. As the Founder of Hausa360 Media and a media technology practitioner, he is passionate about digital journalism, technology reporting, media innovation, and the use of emerging technologies to strengthen information access and public communication.

Exit mobile version