Labaran Dare Na Yau Jumaa 26 Yuni 2026 Hausa360

Saurari cikakken Labaran Dare Na Yau Juma’a 26 June 2026 Hausa360

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 7 ta yanke wa wasu matasa biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin ƙwacen babur da kisan kai a Karamar Hukumar Madobi. Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta yanke wa Hassan Abdullahi da Sani Umar hukuncin ne bayan samunsu da laifin hada baki, fashi da makami da kuma kisan kai. Lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Satumbar 2020 a garin Kubaraci. Kotun ta gamsu da shaidu hudu da lauyan gwamnati ya gabatar.

Karamar Hukumar Tarauni ta ce ta dakatar da aikin gina makarantar da Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tarauni, Alhaji Muktar Umar Yarima, ke shirin aiwatarwa a Hotoro Maraba saboda ba a nemi izini ba kafin fara aikin. Karamar hukumar ta ce filin da ake son gina makarantar a kai tuni ta sahale wa gidauniyar Qatar Foundation. Shugaban kungiyar Kwankwasiyya Hotoro First, Ismail Dau Aliyu, ya ce al’ummar yankin na goyon bayan aikin kuma filin mallakinsu ne.

Shugaban Karamar Hukumar Wase ta Jihar Filato, Dakta Hamisu Mohammed Anani, ya kai tallafin kayan abinci da kudin Naira miliyan 1 ga iyalan wadanda rikicin sarauta ya shafa a Nahuta da ke mazaɓar Kumbur. Rikicin ya faru ne tsakanin al’ummar kabila daya ta Taroh kan takaddamar sarautar gargajiya. Tallafin ya hada da buhunhunan shinkafa, gero, sukari, taliya, man gyada, katifu da N1M. Shugabannin al’ummar Nahuta sun godewa shugaban karamar hukumar tare da alkawarin kauce wa duk wani rikici.

Majiyoyi sun ruwaito cewa ‘yan bindiga sun ƙone wata makarantar firamare da ke garin Dekara a ƙaramar hukumar Borgu ta Niger. Maharan sun ɗauki wannan matakin ne duk da cewa sun karɓi harajin Naira miliyan 10 daga al’ummomin yankin. Mazauna yankin sun shaida wa Daily Trust cewa maharan sun banka wa makarantar firamare ta ‘Central’ wuta. Wani mazaunin yankin ya ce ‘yan bindigar sun fito ne daga dajin Kainji.

Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Joseph Momodu, ya sanar da cewa ya shiga rundunar sojin Amurka. Jarumin ya bayyana hakan a matsayin wata babbar nasara da kuma cikar burin da ya gada daga marigayi mahaifinsa. Momodu ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Juma’a, 26 ga Yuni, 2026. Ya ce ya kammala horon makonni 10 na Basic Combat Training a Fort Leonard Wood da ke jihar Missouri kafin aka dauke shi aiki da mukamin jami’i na musamman (SPC).

Ministan shige da fice na Denmark, Morten Bødskov, ya bayyana cewa gwamnatin kasar na shirin haramta kiran sallah ta amfani da lasifika. Ministan ya ce bai kamata karar kiran sallah da musulmai ke yi akalla sau biyar a kowace rana ya rika tashi a fadin kasar ba. Gwamnati za ta sake bude bincike domin duba yiwuwar samar da tsarin doka. Wasu yankuna na Denmark ciki har da Copenhagen sun riga sun takaita amfani da lasifika saboda dokokin hayaniya.

Jam’iyyar PDP tsagin Tanimu Turaki ta nuna damuwa kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta yanke kan soke rijistar jam’iyyar NDC. Ta ce hakan koma baya ne ga dimokuraɗiyya a Najeriya. Ini Ememobong, sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na riƙo, ne ya fitar da sanarwar. PDP ta ce tana jiran samun cikakken bayani, amma ta yi alawadai da abin da ta kira “murƙushe dimokuraɗiyya” a ƙasar. Ta ce hukuncin ya zo ne bayan ƴan Najeriya da dama sun kashe kuɗaɗe domin neman muƙaman siyasa a ƙarƙashin NDC.

Cristiano Ronaldo ya kasance wanda ya zura ƙwallo a Gasar cin Kofin Duniya daban-daban har shida da ya halarta, tarihin da babu wanda ya kafa shi. Lionel Messi mai shekara 39 ya kafa tarihin yawan cin ƙwallaye a Gasar Kofin Duniya, inda ya ci 18. Lokacin da Ronaldo ya ci Uzbekistan a wasa na biyu a cikin rukuni, ya zama na biyu mafi tsufa da ya taɓa zura kwallo a tarihin gasar, yana da shekara 41 da kwana 138.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

  • Popularly known as Yahmis Yahaya a Media Technology Professional and Journalist with extensive experience in digital media, broadcasting technology, streaming services, and online publishing. He specializes in leveraging technology to enhance news production, content distribution, and audience engagement. As the Founder of Hausa360 Media and a media technology practitioner, he is passionate about digital journalism, technology reporting, media innovation, and the use of emerging technologies to strengthen information access and public communication.

Exit mobile version