Jirgin Ruwan Rasha Ya Ratsa Mashigar Hormuz Duk da Rikici

Wani babban jirgin ruwa mai alaƙa da Rasha ya ratsa Mashigar Hormuz duk da takunkumin da ke tattare da yankin.

Jirgin ruwan mai suna Nord Luxury, mai tsawon mita 142, wanda ake danganta shi da attajirin ɗan kasuwa Alexey Mordashov — kusa da shugaban Rasha Vladimir Putin — ya yi tafiya daga Dubai zuwa Muscat a Oman a ƙarshen mako.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin na daga cikin kaɗan daga cikin jiragen ruwa marasa alaƙa da gwamnati ko kasuwanci da suka samu damar wucewa ta mashigar cikin ƴan watannin nan.

Karanta cikakken labarin: Iran ta sake rufe mashigar Hormuz kan takaddamar da Amurka

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Iran ke ƙara ƙulla alaƙa da Rasha, yayin da ake ci gaba da takun-saƙa tsakaninta da Amurka kan batun buɗe Mashigar Hormuz.

Mashigar Hormuz na da matuƙar muhimmanci a duniya, domin ana kiyasin kusan kashi ɗaya cikin biyar na danyen mai da iskar gas da ake amfani da su a duniya na ratsa ta wannan hanya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version