Gwamnatin Jihar Kano ta karbi bakuncin wata tawaga daga Babban Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Najeriya domin ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa da ci gaba tsakanin ɓangarorin biyu.
Tawagar wadda Ms. Cynthia Rowe, shugabar sashen haɗin gwiwar raya ƙasa ta ofishin jakadancin Birtaniya, ta jagoranta ta kai ziyarar ban girma ne domin duba ayyukan haɗin gwiwa da ake gudanarwa ƙarƙashin tsarin UK-Kano Mutual Accountability Framework.
A yayin ziyarar, an wakilci Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda aka tattauna muhimman fannoni da suka haɗa da gyaran tsarin shugabanci, ilimi, lafiya, bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa cibiyoyi da kuma haɗa kowa cikin harkokin ci gaba.
Bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin gwiwa domin samar da ci gaba mai ɗorewa da inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa dangantaka tsakanin gwamnatin Kano da ƙasashen ƙetare wajen samar da ayyukan raya ƙasa da ci gaban al’umma.
