Gwamnan Kano Ya Nada Sarkin Gaya Amirul Hajj 2026

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Sarkin Gaya, Mai Martaba Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin Amirul Hajj na jihar Kano domin aikin Hajjin shekarar 2026.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an nada Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, a matsayin mataimakin Amirul Hajj domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan hajjin bana.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana sa ran Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano za ta bayar da cikakken goyon baya ga Amirul Hajj da mataimakinsa domin tabbatar da gudanar da aikin hajji cikin nasara da tsari.

Hakazalika, gwamnatin ta yi wa Amirul Hajj da mataimakinsa da ma’aikatan hukumar alhazai fatan nasara tare da addu’ar Allah ya sa maniyyatan jihar Kano su gudanar da aikin hajji lafiya kuma su dawo gida cikin aminci.

Nadin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen aikin Hajjin shekarar 2026 a fadin Najeriya.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version