Reshen Academic Staff Union of Universities na Jami’ar Jihar Gombe (GSU) ya yi kira ga gwamnatin jihar Gombe da ta gaggauta biyan dukkan hakkokin da ake bin mambobinsa, ko kuma su shiga yajin aiki.
Shugaban ASUU na jami’ar, Dr Mustapha S. Shehu, ya ce ana bin malamai bashin alawus-alawus da dama, ciki har da Earned Academic Allowance (EAA) na shekarar 2021 zuwa 2024, da karin albashi na 25% da 35%, da kuma sauran kudaden mafi karancin albashi da aka yi wa alkawari.
Ya ce duk kokarin da kungiyar ta yi na tuntubar gwamnati bai haifar da sakamako ba, wanda hakan ya sa suka zartar da matsaya cewa dole a biya dukkan hakkokin nan da gaggawa.
ASUU ta kuma bukaci aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU a shekarar 2025, tare da biyan karin alawus na koyarwa, horon dalibai, da sauran nau’o’in alawus da ake bin su.
Kungiyar ta gargadi cewa idan gwamnati ta ki daukar mataki, za ta iya daukar wasu matakai da ka iya shafar zaman karatu a jami’ar.
Dr Shehu ya kuma yi kira ga iyaye, masu ruwa da tsaki da al’umma da su shiga lamarin domin ganin gwamnati ta cika alkawuranta.
