Zulum: Mun rufe kasuwar Jilli shekaru biyar da suka wuce

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta rufe kasuwar Jilli tun shekaru biyar da suka gabata, sakamakon zargin cewa ta zama mafakar ƴan ta’adda.

Zulum ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa yayin da yake mayar da martani kan rahotannin wani harin sama da ake zargin rundunar sojin saman Najeriya ta kai, wanda aka ce ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 50 a ranar Asabar.

Ya ce an riga an rufe kasuwar Jilli da kuma ta Gazabure tun da dadewa, yana mai jaddada cewa matakin ya kasance domin dalilan tsaro.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version