A yau ne wa’adin da shugaban Amurka, Donald Trump, ya bai wa Iran domin ta bude mashigar Strait of Hormuz ke karewa.
A ranar Litinin da ta gabata, Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta kai hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa a Iran, ciki har da tashoshin wutar lantarki da gadoji, idan har ƙasar ta ƙi buɗe mashigar.
Tun da farko dai Iran ta yi watsi da shawarar tsagaita wuta na wucin gadi, tana mai jaddada cewa za ta amince ne kawai da kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya na dindindin.
A wani ɓangare kuma, jakadan Iran a Pakistan wadda ke taka rawa wajen shiga tsakani tsakanin Amurka da Iran ya yaba da ƙoƙarin Pakistan na sasanta bangarorin biyu, yana mai cewa yunƙurin dakatar da rikicin na samun wani muhimmin ci gaba.

