Umar Ardo Zai Maka NDC Kotu Kan Zargin Saba Ka’idoji

Dr. Umar Ardo ya bayyana aniyarsa ta maka jam’iyyar NDC a gaban kotu, bayan rahotannin komawar wasu fitattun ‘yan siyasa ciki har da Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi zuwa jam’iyyar.

Ardo ya ce matakin nasa na zuwa ne sakamakon zargin cewa jam’iyyar ta karya wasu ka’idojin da suka shafi tsarinta da yadda take tafiyar da harkokinta na cikin gida.

Ya bayyana cewa zai nemi kotu ta duba sahihancin matakin jam’iyyar, musamman yadda sauye-sauyen da ake zargin sun faru suka shafi tsarin shugabanci da dokokin jam’iyyar.

Har yanzu dai jam’iyyar NDC ba ta fitar da cikakken martani kan zargin da ake mata ba, yayin da al’amuran siyasa ke ci gaba da ɗaukar sabon salo bayan sauye-sauyen da aka samu a cikin manyan ‘yan siyasa.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version