Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa kasarsa na ci gaba da kokarin tsawaita tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, tare da neman hanyoyin rage tashin hankali da tabbatar da ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a yankin.
Erdogan ya bayyana hakan ne yayin jawabi a majalisar dokokin kasar, inda ya ce Turkiyya na cikin tattaunawa da manyan bangarori ciki har da Amurka, Iran, da Pakistan, wadda ke taka rawa wajen shiga tsakani domin hana rikici ya sake barkewa.
Ya kara da cewa duk da akwai kalubale da cikas, har yanzu akwai kyakkyawan fata na ganin an ci gaba da tattaunawa, yana mai jaddada cewa tsagaita wutar da aka samu a yanzu dama ce da ya kamata a yi amfani da ita wajen gina zaman lafiya mai dorewa.
Shugaban na Turkiyya ya kuma yi gargadi kan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Lebanon, inda ya ce hakan na kara dagula ƙoƙarin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rahotanni daga jami’an diflomasiyya sun nuna cewa ana shirin gudanar da taron ministocin harkokin wajen ƙasashe daga Turkiyya, Pakistan, Saudi Arabia da Egypt a birnin Antalya. Ana kuma sa ran Firayim Ministan Pakistan, Shehbaz Sharif, zai halarci taron.
Erdogan ya jaddada cewa idan aka mayar da hankali kan zaman lafiya na dogon lokaci da haɗin kai tsakanin ƙasashe, yawancin matsalolin da ake fuskanta a yanzu za a iya warware su cikin sauƙi.
Turkiyya, Erdogan, Iran, Amurka, tsagaita wuta, diflomasiyya, Pakistan, Shehbaz Sharif, Lebanon, Isra’ila, Gabas ta Tsakiya, zaman lafiya, tattaunawa, labaran duniya, siyasar duniya, Antalya taro, rikicin kasa da kasa, breaking news Hausa, peace talks, international relations
