Trump: An bude mashigar Hormuz, jirage na ci gaba da wucewa

Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya ce an bude Mashigar Hormuz, kuma jiragen ruwa sun fara komawa suna wucewa.

Wannan na zuwa ne bayan tashin hankali da ya biyo bayan barazanar da Iran ta yi na kai hari kan jiragen ruwa a yankin Gulf, Bahar Maliya da Tekun Oman idan Amurka ta ci gaba da toshe tashoshin ruwanta.

A ranar Litinin, Amurka ta sanar da shirin ta na takaita zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa tashoshin Iran, tana mai cewa cikin awa 24 babu wani jirgi da ya ratsa mashigar.

A wata hira da ya yi da Fox News kafin sabbin barazanar Iran, Trump ya ce an buɗe mashigar kuma harkokin sufuri sun fara dawowa yadda aka saba, sai dai bai yi ƙarin bayani ba.

Karanta: Wa’adin da Trump ya bai wa Iran kan mashigar Hormuz ya kare yau

Ya kuma ƙara da cewa har yanzu batun Iran bai ƙare ba, yana mai gargadin cewa rikici na iya ƙara ƙamari, duk da cewa ya nuna buɗe ƙofa ga yiwuwar tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version