Tawagar hukumar kula da fansho ta kasar Afirka ta Kudu ta kai wata muhimmiyar ziyara zuwa matatar mai ta Dangote Group da ke Lagos domin ganin irin ci gaban da kamfanin ya samu a bangaren makamashi da kuma samar da takin zamani.
A yayin ziyarar, tawagar ta zagaya sassan matatar inda suka ga yadda ake gudanar da ayyukan tace mai cikin inganci tare da amfani da sabbin fasahohi.
Sun bayyana cewa aikin matatar zai taimaka wajen rage karancin man fetur a nahiyar Afirka tare da karfafa tattalin arziki.
Har ila yau, tawagar ta yaba da irin gudunmawar da kamfanin ke bayarwa wajen samar da ayyukan yi ga dubban mutane da kuma bunkasa masana’antu a Najeriya da sauran kasashen Afirka.
Sun ce irin wadannan manyan ayyuka na nuna cewa nahiyar Afirka na da damar ci gaba idan aka samu zuba jari mai kyau da tsari nagari.
