Hukumomi a Saudiyya sun dakatar da yin sallah a dukkan masallatan kasar, idan ban da masallacin Ka’abah da kuma na Madina waton Masallacin Manzon Allah sira da amincin Allah su tabbata agareshi, a cewar kamfanin dillacin labaran kasar wato Saudi Gazette.
A baya dai mahukuntan Saudiyya sun hana masu zuwa aikin Umrah da na Hajji shiga kasar saboda yaduwar cutar coronavirus.
An dauki matakin ne makonni kadan kafin azumin watan Ramalana inda Musulmi kan yi tururuwa zuwa kasar domin gudanar da ayyukan ibada.
Kawo izuwa yanzu, mutane 133 aka tabbatar sun kamu da cutar a Kasar Saudiyyan.