Mahukuntan kasar Saudiyya sun sanar da ranakun da za a gudanar da hawan Arfa da kuma bikin Babbar Sallah na bana bayan kammala duba jinjirin watan ZulHijjah.
A cewar sanarwar da aka fitar, ranar 26 ga watan nan za ta kasance ranar Arfa, yayin da ranar 27 za ta kasance ranar Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi.
Sanarwar ta zo ne bayan tabbatar da ganin watan a wasu sassan kasar.
Musulmai daga sassa daban-daban na duniya na ci gaba da shirye-shiryen gudanar da ibadun Hajji da kuma bukukuwan Sallah, yayin da mahajjata ke ci gaba da taruwa a birnin Makkah domin gudanar da manyan ibadun aikin Hajji.
