Rahotanni na cewa an bai wa Nasir El-Rufai beli daga Kotun Tarayya

Rahotanni daga Freedom Radio na cewa an bai wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, beli daga Kotun Tarayya. A cewar rahoton, kotun ta amince da bukatar belin da lauyoyinsa suka gabatar bayan sauraron shari’ar, inda aka ba shi damar fita bisa wasu sharudda, duk da cewa har yanzu ba a bayyana cikakkun sharuddan ba. Sai dai kawo yanzu, babu tabbaci daga manyan kafafen yaɗa labarai ko wata sanarwa a hukumance dangane da wannan batu. Ana sa ran El-Rufai zai ci gaba da fuskantar shari’ar da ake yi a kansa a gaban kotu. Za mu ci gaba da kawo muku ƙarin bayani da zarar an samu tabbaci daga sahihan majiyoyi.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version