NNPC ta kammala aikin bututun gas a Kogin Neja

NNPC Limited ta sanar da kammala muhimmin aikin ketare Kogin Neja a bututun iskar gas na Obiafu-Obrikom-Oben (OB3), wanda ke zama babban ci gaba a tsarin rarraba iskar gas na Najeriya.

Aikin da reshen kamfanin, NNPC Gas Infrastructure Company (NGIC) ya kammala, ya bude hanyar cikakken amfani da bututun OB3 mai tsawon kilomita 130, wanda aka tsara zai iya daukar iskar gas har biliyan 2 na cubic feet a kowace rana.

An aiwatar da aikin ne ta karkashin Kogin Neja a zurfin kusan kilomita biyu ta amfani da fasahar zamani ta “horizontal directional drilling (HDD)” tare da hadin gwiwar kamfanin PCE Nig. Limited.

Shugaban rukunin NNPC, Bayo Ojulari, ya ce wannan nasara babbar hujja ce ta ingantaccen aiki da kwarewa wajen aiwatar da manyan ayyukan kasa.

Ya ce kammala aikin zai inganta samar da iskar gas, kara dorewar wutar lantarki, da kuma habaka ci gaban masana’antu a Najeriya.

Ojulari ya kara da cewa nasarar ta ginu ne kan kwarewar da aka samu daga aikin AKK da aka kammala a baya, wanda ya taimaka wajen kara inganta dabarun injiniya da gudanar da ayyuka.

Ya gode wa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu bisa goyon bayan manufofin “Gas-to-Prosperity”, da kuma kwamitin gudanarwar NNPC da sauran masu ruwa da tsaki.

Haka kuma ya yaba wa al’ummomin da ke yankin aikin da kuma kamfanin PCE Nig. Limited saboda gudunmawar da suka bayar wajen kammala wannan muhimmin aikin kasa.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version