Hukumar National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) a jihar Edo State ta kama kilogiram 1,378 na tabar wiwi (Cannabis Sativa) a wani samame da ta kai kan wata ma’adanar haramtacciyar kaya.
A yayin aikin, jami’an hukumar sun kama wani mutum mai suna Roland Owie, mai shekaru 37, wanda ake zargi da kasancewa mamba a cikin wata Kungiyar dillalan miyagun ƙwayoyi.
Rahotanni sun bayyana cewa an kai samamen ne a unguwar Igbanke da ke Karamar hukumar Orhionmwon bayan samun sahihin bayanan sirri.
Karanta Kotun Tarayya Ta Wanke Abba Kyari
Shugaban NDLEA na jihar, Mitchel Ofoyeju, ya bayyana cewa an kwace buhuna 125 na tabar wiwi da aka boye a cikin wani sito, wanda ya kai jimillar nauyin kilogiram 1,378.
Ya ce wannan nasara ta taimaka wajen katse hanyoyin rarraba miyagun Kwayoyi zuwa makarantu da al’umma, tare da rage barazanar shaye-shaye a tsakanin matasa.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da farmakin ta kan masu safarar miyagun Kwayoyi domin rage tasirinsu a cikin al’umma.
