Nasir El-Rufai ya maka ICPC a kotu

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya shigar da kara a kan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, kamar yadda mai magana da yawunsa, Muyiwa Adekeye, ya wallafa a shafinsa na X.

El-Rufai ya kai ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda yake neman kotu ta ayyana takardar izinin binciken da aka yi a gidansa a matsayin mara inganci, tare da bayyana cewa an tauye masa haƙƙinsa na ɗan ƙasa.

Haka kuma ya roƙi kotun ta umarci hukumar da ta mayar masa da kayayyakin da aka kwashe daga gidansa, tare da hana ta amfani da su a nan gaba.

Rahotanni sun nuna cewa a halin yanzu El-Rufai na hannun ICPC, wadda ta je gidansa domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake masa na aikata wasu laifuka.

Tun da farko, Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ce ta fara tsare shi, kafin daga bisani a mika shi hannun ICPC, wadda ita ma ke gudanar da nata binciken daban.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.
Exit mobile version