Masu goyon bayan Shamsuddeen Bala Mohammed sun ce rahoton da ke yawo na neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu ƙirƙira ne kuma ba shi da tushe.
A cikin sanarwar sunce Hankalinmu ya karkata ga wani rubutu da Jaridar Najeriya ta wallafa, wanda ke ɗauke da kalamai da aka jingina ga Engr. Shamsuddeen Bala Mohammed dangane da takarar kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu.
Zan yi amfani da wannan dama na bayyana karara cewa, Babu wata gardama ko tantama cewa wannan magana ba gaskiya ba ce! ƙirƙirarriya ce tsagwaronta!! Engr. Shamsuddeen Bala Mohammed bai taɓa yin irin wannan furuci ba a kowane lokaci.
A nan dole na bayyana takaici bisa yadda aka ɗauki salon kirkirar magana tare da jingina ta ga mutum, domin haifar da rudani da karkatar da fahimtar jama’a ko kuma kawai don batanci. Wannan ba aikin jarida na gaskiya ba ne, illa sakaci da rashin bin ƙa’idojin sahihanci da tabbatar da bayanai kafun wallafawa
Don kauce wa duk wani ruɗani, ya zama dole mu sake jaddada sahihin manufa da kuma tabbatar da cewa ainihin abin da Engr. Shamsuddeen Bala Mohammed yake da kudirin a kai, sannan a halin yanzu yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci da Engr. Shamsudden ya mai da hankali akan su. Wato karfafar matasa ta ko wani janibi na rayuwa da mutum ya zaba!
Shaharudden Bala Mohammed ya mai da hankali ne wajen ƙarfafa matasa a fannoni daban-daban na rayuwa, kama daga ilimi, sana’o’i, kasuwanci da sauran hanyoyin dogaro da kai. A duk inda ya ga matashi mai buri da ƙwazo, yana ƙoƙarin tallafa masa gwargwadon iko domin ya samu ci gaba mai ɗorewa.
Saboda haka, yunƙurin mayar da wannan manufa zuwa batun siyasa ko zaɓe, musamman danganta shi da Neman kujerar Sanatan Bauchi ta Kudu ko ta halin kaka, ba daidai ba ne kuma ya saba da gaskiyar lamarin wannan Dantalikin.
Muna kuma bayyanawa a sarari don al’ummah su kwan da sani cewa, batun takarar kujerar Sanata ba shi ne a gaban Engr. Shamsuddeen Bala Mohammed a wannan lokaci ba. Duk wani iƙirari da ke nuna akasin haka, batu ne kawai mara tushe bare makama.
Muna kira ga Jaridar Najeriya da ta duba al’amarin nan da muhimmanci, tare da gyara kuskuren da aka yi domin kare martabar aikin jarida da kuma samun aminci daga bangaren jama’a.
Haka kuma, muna kira ga al’umma da su yi taka-tsantsan da bayanan da ba su da tushe, su kuma rika tabbatar da sahihancin zance kafun yaɗawa.
Daga Karshe sukace Ku sani fa Haja mai kyau bata bukatar Talla, kuma duk rintsi Gaskiya bata buya!!!
