Kwamitin Majalisar Wakilan Amurka ya gabatar da wani kuduri da ke neman a dauki mataki kan zargin musguna wa Kiristoci da kuma ayyukan wasu kungiyoyin yan bindiga a Najeriya.
Kudirin, mai taken “Nigeria Religious Freedom and Accountability Act,” ya bukaci Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya rika gabatar wa kwamitocin harkokin wajen majalisa rahoto duk shekara kan matakan da ake dauka domin magance zargin take hakkin addini a Najeriya.
Haka kuma, kudurin ya nemi a tantance yiwuwar ayyana wasu kungiyoyi da ake dangantawa da “makiyaya Fulani” a matsayin kungiyoyin ta’addanci na kasashen waje. Bugu da kari, ya bukaci a sanya takunkumi kan wasu mutane da ake zargi da hannu a cin zarafin Kiristoci.
Domin kudurin ya zama doka, dole ne ya samu amincewar duka majalisun dokokin Amurka.
Wannan mataki na zuwa ne bayan Amurka ta sanar da shirin tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin kasar kan dabarun yaki da masu tayar da kayar baya. Ana sa ran za su iso cikin makonni masu zuwa, inda za su hadu da wata karamar tawaga da aka riga aka tura a baya.
Kakakin rundunar sojin Najeriya, Janar Samaila Uba, ya tabbatar da shirin ga BBC, yana mai cewa hakan ya biyo bayan gayyata da bukatar gwamnatin Najeriya, kuma ya yi daidai da shawarwarin kwamitin hadin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya.
