Kwamitin kasafin kuɗi na United States Congress ya gabatar da wani ƙudirin doka da ke neman a dakatar da tallafin da ake bai wa Nigeria har sai an magance matsalolin hare-hare a sassan ƙasar, musamman da ke shafar ‘yan ƙasa.
Ƙudirin ya fi mayar da hankali kan tallafin tsaro da shirye-shiryen kasafin kuɗi na shekarar da za ta ƙare a ranar 30 ga Satumba, 2027.
Ɗan majalisa Riley Moore ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kashe miliyoyi wajen neman goyon bayan majalisar, amma ta gaza magance matsalar da ake zargin na kisan Kiristoci a ƙasar.
Ya ce ba za su amince su rufe ido ba yayin da ake zargin ana ci gaba da kashe Kiristoci a Najeriya.
Ƙudirin ya tanadi cewa kashi 15 cikin 100 na dala biliyan 6.89 da aka ware domin tsaro a Afirka za su tafi ne wajen yaƙi da ta’addanci, inda aka ware dala miliyan 870 domin wannan aiki.
Haka kuma, ƙudirin ya ce ba za a fitar da kashi 50 na kuɗin da aka ware wa Najeriya ba har sai an tabbatar da cewa an ɗauki matakan hana rikici da kuma hukunta masu laifi.
Sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken adadin kuɗin da aka ware kai tsaye ga Najeriya ba a cikin ƙudirin.
