Kotun Koli Zata Yanke Hukunci Kan Rikicin ADC

Kotun Koli ta Najeriya za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC tsakanin David Mark da Nafi’u Bala a ranar Alhamis da karfe 2 na rana.

Kotun Koli ta Najeriya ta sanya ranar gobe Alhamis a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan rikicin shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), wanda ya kunno kai tsakanin bangaren Sanata David Mark da kuma bangaren Nafi’u Bala.

Kotun ta sanar da bangarorin biyu cewa za ta zauna domin yanke hukuncin da misalin karfe 2:00 na rana.

KarantaADC ta ayyana 12 ga Mayu don rantsar da sabbin shugabanninta

A makon da ya gabata ne kotun ta dage sauraron shari’ar, bayan da ta kammala sauraron dukkan hujjoji da bayanan bangarorin biyu, lamarin da ya sa ake jiran hukuncin karshe domin fayyace wanda ke da halastacciyar shugabanci a jam’iyyar.

Domin Sumun Labari, Rahotanni da dumi dumin su shiga WhatsApp: Hausa360 WhatsApp Group Twitter : Hausa360 Twitter Facebook: Hausa360 Facebook Instagram : @Hausa360 YouTube: @Hausa3600 domin gani da ido a zahiri da sauran nishadi.

Author

Exit mobile version