Gwamnatin Tarayya ta sauya zarge-zargen da take yi wa tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdul’aziz, inda aka cire zargin ɗaukar nauyin ta’addanci.
A zaman kotu na ranar Laraba, wakilin hukumar DSS, Akinlolu Kahinde, ya sanar da kotu cewa an sauya tuhumar, tare da maye gurbin wasu daga cikin zarge-zargen.
Daga cikin sauye-sauyen akwai cire zargin mallakar makamai.
Lauyan Malami, Shu’aibu Aruwa, ya tabbatar da cewa wanda yake karewa ya amince da sabbin tuhumomin da aka gabatar bayan an karanta su a kotu.
Karanta: Hukumar DSS ta bude shafukan sada zumunta dan yin aiki
Tun da farko dai Malami ya musanta dukkan zarge-zargen da aka yi masa.
Kotun ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Mayu da kuma 15 ga watan Yuni.
