Fitacciyar jarumar masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Wasila Isma’il, ta rasu bayan fama da rashin lafiya a jihar Kaduna da safiyar yau Lahadi 24 ga watan mayu 2026.
Makusantan marigayiyar sun bayyana cewa Wasila Isma’il ta rasu ne bayan jinya da ta shafe lokaci tana yi.
Rahotanni sun ce ta bar ƴaƴa hudu a duniya, mata uku da namiji daya.
Rasuwar jarumar ta jawo alhini a tsakanin masoya fina-finan Hausa da abokan aikinta a masana’antar Kannywood.
Wasila Isma’il na daga cikin tsofaffin jaruman Kannywood da suka yi fice a shekarun farko na bunkasar fina-finan Hausa.
Ta yi suna sosai a cikin fim din “Wasila” wanda aka saki a shekarar 2000. Fim din ya samu karbuwa sosai a Arewacin Najeriya kuma ya taimaka wajen kara daukakarta a masana’antar Kannywood.
A cikin fim din, ta fito tare da fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Hajara Usman da sauran manyan taurarin Kannywood. Masana’antar ta tuna ta a matsayin daya daga cikin jaruman mata da suka taimaka wajen kafa tubalin fina-finan Hausa.
Wasila Isma’il ta shahara wajen fitowa a fina-finan soyayya da na zamantakewa. Masoya Kannywood da dama sun bayyana ta a matsayin jaruma mai hazaka da nutsuwa a lokacin aikinta. Wasu daga cikin fina-finanta sun mayar da hankali ne kan rayuwar aure, soyayya, da matsalolin iyali da ke faruwa a cikin al’umma.
Tun bayan bayyana rasuwar tata, mutane da dama a kafafen sada zumunta suna bayyana alhininsu tare da yi mata addu’ar samun rahama. Masoya fina-finan Hausa sun bayyana rasuwar tata a matsayin babban rashi ga masana’antar Kannywood.
Rasuwar Wasila Isma’il ta bar gibi a masana’antar fina-finan Hausa, musamman ga wadanda suka taso suna kallon fina-finanta tun farkon shekarun Kannywood. Masoya da abokan aikinta na ci gaba da yi mata addu’ar Allah ya jikanta da rahama.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.”
