Jam’iyyar (PDP) mai Mulki a Jihar Bauchi ta bayyana cewa ta dakatar da tattaunawar siyasa da take yi da jam’iyyar (APC).
Shugaban jami’iyar PDP na jihar Bauchi, Alhaji Sama’ila Adamu Burga, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke kan titin Yandoka a Bauchi.
Ya ce an shirya taron ne domin sanar da al’umma halin da ake ciki dangane da jam’iyyar, shugabancinta da kuma manyan masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, tattaunawar ta biyo bayan gayyatar da APC ta miƙa wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, da ‘yan PDP da sauran zaɓaɓɓun jami’ai domin su duba yiwuwar komawa jam’iyyar mai mulki.
Ya bayyana cewa gwamnan da shugabannin PDP sun shiga tattaunawar da kyakkyawar niyya, bisa manufar tattaunawa da haɗin kai.
Sai dai ya ce bayan tuntuba da shawarwari, sharuɗɗan da jami’iyar APC ta gabatar, musamman kan tsarin jam’iyya da rabon mukaman madafun iko, jami’iyar PDP a jihar Bauchi bata aminta da su ba.
Saboda haka, Alhaji Burga ya sanar da cewa ba’a kai ga cimma matsaya ba, kuma an kawo ƙarshenta a hukumance.
Yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, ya ce jam’iyyar na sane da lokutan zaɓe, kuma za ta ɗauki duk matakan da suka dace domin bin doka ba tare da barin wani abu a baya ba.
Ya ƙara da cewa PDP za ta ci gaba da nazarin hanyoyin siyasa daban-daban domin kare muradun ‘ya’yanta da al’ummar Jihar Bauchi baki ɗaya.
